Isa ga babban shafi
Spain

Shugabannin Barcelona sun yi murabus

Shugabannin gudanarwar kungiyar Barcelona sun bayyana yin murabus a wani mataki na bude kofar gudanar da sabon zaben shugabannin da zasu tafiyar da kungiyar. Shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya shaidawa manema labarai a yau Talata cewa ya ajiye mukaminsa domin bayar da damar zaben sabon shugaban da zai jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 6.

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu
Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Mambobi dubu 153 ke da hakkin tafiyar da kungiyar wadanda kuma ke zabar shugabanni, sabanin sauran kungiyoyin kwallon kafa da kamfanoni masu zaman kansu ko attajira ke kula da ikon tafiyar da su.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da kocin kungiyar ya amince da yarjejeniyar tsawaita kwangilar shi ta tsawon shekaru biyu.

Haka kuma Dani Alves ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekaru biyu da Barcelona wanda ya kawo karshen rade radin dan wasan zai fice kungiyar bayan ya shafe shekaru sama da 7 yana taka leda a kungiyar da ta yi bikin lashe kofuna uku a bana.

Alves zai ci gaba da bugawa Barcelona kwallo har zuwa 2017.
A shekarar 2008 ne Barcelona ta karbo Alves daga Sevilla, kuma dan wasan zuwa yanzu ya yi haskawa 343 a Barca, wanda shi ne dan wasa daga wata kasa da yi fi yawan haskawa a kungiyar.

Alves ya lashe wa Barcelona kofuna 19, da suka hada da La liga 5 da kofin zakarun Turai 3 da Copa Del Rey 2

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.