Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter zai kauracewa wasan Mata a Canada

Shugaban FIFA Blatter ba zai halarci wasan karshe na gasar cin kofin Mata ba da ake gudanarwa a Canada, kamar yadda lauyansa ya tabbatar a jiya Talata.

Joseph Blatter Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya
Joseph Blatter Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya © Reuters
Talla

Wannan ne kuma karon farko da shugaban na hukumar kwallon kafa ta duniya zai kauracewa wasan karshe da zai hannuna kofi ga wanda ya samu nasara a gasa, tun zabensa na farko a matsayin shugaban hukumar a 1998.

Ana ganin dai wannan bai rasa nasaba da rikicin rashawa da ya shafi FIFA a karkashin jagorancinsa, lamarin da har ya sa zai yi murabus.

Amma lauyan da ke kare Blatter ya ce, shugaban na FIFA zai kauracewa wasan na mata ne saboda ayyukan da su kai ma shi yawa a hedikwatar hukumar FIFA.

A ranar 2 ga Yuni ne Blatter ya bayyana cewa zai yi murabus a babban taron FIFA da za a gudanar a watan Disemba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.