Isa ga babban shafi
Wimbledon

Serena za ta hadu da Sharapova a Wimbledon

Serena Williams ta tsallake zuwa zagayen kusa da karshe a gasar Wimbledon bayan ta doke Victoria Azerenka a kwata fainal. A gobe Alhamis Serena za ta hadu ne da Maria Sharapova da ta dade tana ba kashi a haduwarsu.

Serena Williams of the U.S.A. celebrates after winning her match against Victoria Azarenka of Belarus at the Wimbledon Tennis Championships in London, July 7, 2015.
Serena Williams of the U.S.A. celebrates after winning her match against Victoria Azarenka of Belarus at the Wimbledon Tennis Championships in London, July 7, 2015. REUTERS/Toby Melville
Talla

A daya bangaren kuma Garbine Muguruza ta Spaniya zata kara ne da Radwaska ta Poland a zagayen kusa da karshe.

A yau Laraba manyan jaruman Tennis guda hudu Novak Djokovic da Roger Federer da Andy Murray da Stan Wawrinka za su yi kokarin tsallakewa zuwa zagayen kusa da karshe a gasar Wimbledon da ake gudanarwa a Birtanitya.

Djokovic da ke kokarin kare kofin gasar zai fafata ne da Marin na Croatia wanda ya lashe kofin US Open.

Roger Federer kuma zai kara ne da Gilles Simon na Faransa, Andy Murray na Birtaniya kuma zai hadu ne da Vasek Pospisil na Canada.

 

Wawrinka wanda ya lashe Roland Garros zai kece raini ne da Richad Gasquest na Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.