Isa ga babban shafi
Audi

Bayern Munich ta lashe kofin Audi a Jamus

Bayern Munich ta lashe kofin Audi bayan ta doke Real Madrid ci 1 da 0 a fafatawar soma kakar wasanni da suka yi a jiya Laraba. Robert Lewandowski ne ya jefa wa Bayern Munich kwallonta a ragar Real Madrid ana saura minti biyu a hure wasan.

Bayern Munich ta doke Real Madrid a gasar lashe kofin Audi a Jamus
Bayern Munich ta doke Real Madrid a gasar lashe kofin Audi a Jamus REUTERS/Michaela Rehle
Talla

Sau uku ke nan da Bayern Munich na lashe kofin na Audi a karo hudu tun kaddamar da kofin gasar a 2009.

Tottenham ce ta zo a matsayi na uku a gasar bayan ta doke AC Milan 2-0.

Bayern Munich da Real Madrid da AC Milan da Tottenham ne suka fafata a gasar lashe kofin na Audi a Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.