Isa ga babban shafi
wasanni

Gary Lineker yace watakila Rooney ya dade yana jan zarensa

Tsohon Shahararren dan wasan kwallon kafan kasar Ingila, Gary Lineker yace yana gani za a dauki tsawon lokaci kafin a sami dan wasan da zai shafe tarihin da Wayne Rooney ya kafa, bayan da ya ciwo wa kasar kwallonsa ta 50, yayin wasan da suka yi da kasar Switzerland ranar Talata.

Dan wasan kasar Ingila da Manchester United, Wayne Rooney
Dan wasan kasar Ingila da Manchester United, Wayne Rooney Action Images/Reuters/Carl Recine
Talla

Wannan ne ya dora Rooney a gaban Bobby Charlton, da ya ciwo wa kasar kwallaye 49, kuma aka shafe shekaru 49 ba a sami wanda ya shafe wancan tarihin ba, sai ranar ta Talatan.
Dama shi kuma Lineker nada kwallaye 48 da ya ciwo wa Ingilan, a lokacin da yake fagen wasa.
Lineker na ganin cewa tunda har yanzu Rooney mai wasa a kungiyar Manchester United, da kuma shine kaftin din ingila, bai cika shekaru 30 kuma watakila ya dade yana taka leda, to zai dade yana jan zarensa a wannan bangaren.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.