Isa ga babban shafi
Wasanni

Hayatou zai jagoranci shugabancin FIFA

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika Issa Hayatou zai jagoranci hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA na wucen gadi.

Issa Hayatou
Issa Hayatou AFP PHOTO / FABRICE COFFRINI
Talla

Wannan na zuwa ne bayan matakin da kwamitin da’a na hukumar FIFA ya dauka na dakatar da Sepp Blatter har na tsawon watanni uku a matsayin shugaban hukumar ta FIFA sakamakon zarginsa da hannu a badakalar cin hanci da rashawa a hukumar.

Har ila yau kwamitin ya dakatar da Michel Platini, shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai saboda zargin da shi ma ake masa na karban kudade daga hannun Blatter ba bisa ka’ida ba.

Hayatou dai mai shekaru 69, ya karbi ragamar FIFA ne a matsayinsa na babban mataimakin Sepp Blatter.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.