Bayern Munich ta lallasa Arsenal
Kungiyar Bayern Munich ta lallasa Arsenal da ci 5-1 a gasar cin kofin zakarun Turai, lamarin da ya haifar da babban kalubale ga Aresnal dangane da kai wa ga ci a rukunin F na gasar.
Wallafawa ranar:
Kocin Arsenal Arsene Wenger ya caccaki 'yan wasansa saboda ba su taka rawar gani ba, inda ya ce sun gaza kare gida har Bayern Munich ta zura kwallaye a ragarsu.
Dan wasan Bayern Munich Thomas Mueller ne ya zura kwallaye biyu a ragar Arsenal yayin da Lewandowski da Alaba da Robben ko wannen su ya zura kwallo guda guda.
Yanzu haka, Arsenal da Dinamo Zagreb na da maki uku uku a rukunin na F, inda kuma Bayern Munich da Olympiakos ke da maki tara tara amma Bayern Munich ne ke saman teburi saboda ta zarce Olympiakos da kwallo guda.
Matukar Arsenal dai na bukatar ta kai matakin gaba, to lallai sai ta samu nasara a wasanni guda biyu da za ta yi nan gaba da Dinamo Zagreb da kuma Olympiakos.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu