TP Mazembe ta lashe kofin zakarun Afrika
Kungiyar TP Mazembe ta lashe kofin gasar zakarun Afrika bayan ta doke USM Alger ta Algeria da jimillar kwallaye 4 da 1. A jiya Lahadi Mazembe ta doke Alger ne 2 da 0 a fafatawar da suka yi a Jamhuriyyar Congo bayan ta samu nasara a karshen makon da ya gabata ci 2 da 1 a Algeria.
Wallafawa ranar:
Wannan ne karo na biyar da TP Mazembe ke lashe kofin gasar zakarun Afrika. Yanzu kungiyar ta yi kafada da Zamlek ta Masar, wadanda ke bayan Al Ahly da ta lashe kofin sau 8.
Kungiyar TP Mazembe ita za ta wakilci Afrika a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa a duniya da za buga a Japan, inda kungiyar za ta gamu da irinsu Barcelona.
A 2010 Mazembe ta buga wasan karshe da Inter Milan a gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa na duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu