Benitez zai ci gaba da horar da Real Madrid
Kocin Real Madrid Rafeal Benitez ya samu cikakken goyon bayan shugaban kungiyar Florentino Perez, kan ci gaba da aikinsa bayan Barcelona ta zane su ci 4 da 0.
Wallafawa ranar:
Tun bayan kammala wasan Clasico a ranar Assabar, magoya bayan Real Madrid da jaridun wasanni masu goyon bayan kungiyar ke kiran a sallami Benitez.
A jiya Litinin kuma shugaban kungiyar Florentino Perez ya shaidawa manema labarai goyon bayan shi ga Benitez bayan shugabannin Real Madrid sun tattauna.
A watan Yuni ne Real Madrid ta dauki Benitez, bayan ta sallami Ancelotti, yanzu kuma tazarar maki 6 Barcelona taba kungiyar a La liga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu