Gasar Turai: Arsenal da Chelsea sun kai matakin gaba
Kungiyoyin kwallon kafa na Arsenal da Chelsea sun tsallaka zuwa matakin gaba na kungiyoyi 16 da za su ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai bayan sun samu nasara a wasanninsu na jiya.
Wallafawa ranar:
Arsenal ta doke Olympiakos da ci 3-0 yayin da Chelsea ta casa FC Porto da ci 2-0.
Tuni dai kocin Chelsea Jose Mourinho ya yi fatan cewa, nasarar da kungiyarsa ta samu za ta maido wa ‘yan wasansa da kuzarinsu da suka rasa a baya, wanda hakan ne ya ke ganin zai taimaka masa har ya ci gaba da zama a matsayin Coci a kungiyar.
Chelsea dai ta gamu da koma baya matuka a wannan kakar, abin da ya sa ake ganin za a iya koran sa daga kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu