Isa ga babban shafi
Wasanni

Al Ahly ta Masar ta dauki Martin Jol a matsayin kocinta

Kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly da ke Masar ta sanar da daukan Martin Jol a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta, inda ya maye gurbin Abdel Aziz Abdel Shafy wanda ya jagorance ta a matsayin kocin rikon kwarya. 

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly Martin Jol.
Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Al Ahly Martin Jol. bestyle.club
Talla

Sanarwar dai na zuwa ne bayan Jol mai shekaru 60 ya amince da kulla kwantiragi da kungiyar, kuma tuni ya gana da shugabanta Mahmoud Taher a birnin London a cikin wannan makon.

Martin Jol dai ya horar da Fulham gabanin ya raba gari da ita a watan Disamban shekarar 2013 bayan ta sha kashi a wasanni shida a jere a gasar Premier ta Ingila.

Sannan ya horar da Tottenham da Ajax da kuma Hamburg ta Jamus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.