Isa ga babban shafi
Wasanni

An shiga zagaye na biyu a zaben FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta shiga zagaye na biyu a zaben da ta ke gudanarwa  domin tsayar da wanda zai maye gurbin Sepp Blatter yayin da ta samar da sauye sauye domin ci gaban hukumar wadda ta yi fama da badakalar cin hanci da rashawa.

FIFA na gudanar da zaben shugabanta a birnin Zurich.
FIFA na gudanar da zaben shugabanta a birnin Zurich. REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Sakamakon zagayen farko na zaben ya nuna cewa Ginanni Infantino ke kan gaba wajan yawan kuri’u inda ya ke da kuri’u 88, yayin da Sheik Salman bin Eibrahim al-Khalifa ke biye masa da kuri’u 85.

Sai kuma yarima Ali na Jordan da ya samu kuri’u 27 yayin da Jerome Champagne ke da kuri’u bakwai kacal.

Tuni dai Tokyo Sexwale na Afrika ta kudu ya janye daga takarar tun kafin a fara kada kuri’u.

A bangare guda, kafin a fara, hukumar ta fitar da wasu sauye sauye, inda ta takaita wa’adin shugabancinta zuwa uku.

Sannan kuma wani sabon kwamitin zartarwa zai maye gurbin kwamitin zartarwa na yanzu, kuma zai kunshi mace guda daga kowace hukumar kwallon kafa ta nahiya.

Kasashe 207 ne ke kada kuri'ar a zaben na yau.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.