Dan wasan Super Eagles John Ene Okon ya rasu
Tsohon dan wasan Tsakiya a Super Eagles John Ene Okon wanda ke cikin tawagar ‘yan wasan kasar da suka buga Chile 87 ya rasu.
Wallafawa ranar:
Okon wanda ke tare da Super Eagles a lokacin da ta zo na 3 a wasan cin kofin Nahiyar Afrika a shekarar 1992, ya rasu a jiya talata yana da shekaru 47 a garin Calabar dake Cross Rivers.
Tsoffi da sabbin ‘Yan wasa da dama na cigaba da bayana alhininsu da wannan rashi na hazikin dan wasan
A shekarar da Chile ta karbi bakwanci wasan cin kofin duniya na Matasa a 1987, Okon ne ya fara ci wa Najeriya kwallon farko, a ci 2-2 da sukayi da Canada.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu