Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal na zargin kanta da rashin kokari

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta zargi kanta da rashin taka rawar gani bayan ta yi nasara a wasanni biyu cikin tara da ta yi a gasa daban daban.

Lokacin da Arsenal ta yi wasa da Barcelona a filin wasa na Emirate a gasar zakarun Turai.
Lokacin da Arsenal ta yi wasa da Barcelona a filin wasa na Emirate a gasar zakarun Turai. REUTERS
Talla

Dan wasanta na tsakiya Mesut Ozil ya bayyana cewa, kamata kungiyar ta ga laifin kanta sakamakon wannan halin da ta tsinci kanta a ciki.

Aresnal dai ta doke Leicester city mai jagorantar teburin gasar Premier da ci 2-1 a ranar 14 ga watan Fabarairu amma Barcelona ta yi waje da ita a gasar cin kofin zakarun Turai.

Sannan kuma Watford ta sake yin waje da ita a gasar cin kofin FA.

Ozil dan asalin kasar Jamus ya jaddada cewa matukar Aresnal ta kammala kakar wasanni ba tare da samun komai ba, to lallai fa sai dai ta zargi kanta da yin sakaci.
 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.