Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya za ta dauko koci daga kasar waje

Kwamintin gudanarwa na hukumar kwallon kafa ta Najeriya zai gana da ministan wasanni da matasa na kasar, Barista Solomon Dalung a ranar Talata mai zuwa, inda za su zanta akan dalilan da suka hana Najeriya samun nasarar shiga gasar cin kofin Afrika da za a gudanar a Gabon a shekara mai zuwa.

Ministan wasanni da matasa na Najeriya, Barista Solomon Dalung
Ministan wasanni da matasa na Najeriya, Barista Solomon Dalung RFI/bashir
Talla

Ana sa ran shugabannin hukumar za su zanta akan yiwuwar dauko kwararren koci daga kasar waje domin horar da tawagar Najeriya ta Super Eagles.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Amaju Pinnick ya fada wa manema labarai cewa, a ranar Talata, za su tsayar da shawara akan ko dai su amince da dan Najeriya ya ci gaba da horar da Super Eagles, ko kuma su dauko wani daga kasar waje.

A ranar Talatar da ta gabata ne, kasar Masar ta haramta wa Najeriya zuwa gasar cin kofin Afrika a Gabon bayan ta doke ta da ci daya mai ban haushi a fafatawar da su ka yi a Masar.

Ko a shekarar bara dai, Najeriyar ba ta samu damar shiga irin wannan gasar ba wadda aka gudanar a Equitorial Guinea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.