Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Wasan fita kunya a bana za mu buga da Wolfsburg-Zidane

Kocin real Madrid Zinedine Zidane ya danganta wasansu da Wolfsburg a ranar Talata a gasar zakarun Turai, a matsayin wasan fita kunya a wannan kakar ta bana.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane Reuters/Fabian Bimmer
Talla

Zidane ya fadi haka ne a yau Juma’a, bayan Real Madrid ta sha kashi ci 2 da 0 a gidan Wolfsburg a ranar Laraba.

Zidane ya bayyana kwarin guiwarsa akan zasu sauya sakamakon wasan musamman saboda goyon bayan da za su daga magoya bayansu a gida Santiago Bernabeu domin tsallakewa zuwa zagayen kusa da karshe.

Zidane ya ce bai damu da abin da zai faru da makomarsa ba idan har Wolfsburg ta fitar da Real Madrid.

Amma ya ce yan sann komi na iya faruwa da aikin shi idan har ya bari ya sake shan kashi a makon gobe.

Kofin gasar zakarun Turai ne dai Real Madrid ta sa a gaba a kakar bana bayan an kori kungiyar a gasar Copa del Ray, kuma kofin La liga ya yi Zidane nisa domin maki 7 ne Barcelona ta ba Real Madrid a teburin gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.