Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

An hada City da Madrid, Bayern da Atletico

An hada Manchester City da Real Madrid a zagayen dab da na karshe a gasar zakarun Turai yayin da kuma aka hada Atletico Madrid da Bayern Munich.

A Milan za a yi wasan karshe a bana
A Milan za a yi wasan karshe a bana REUTERS
Talla

City ce zata fara karbar bakuncin Madrid, Bayern Munich kuma zata fara kai wa Atletico Madrid ziyara ne a wasannin da kungiyoyin hudu zasu fafata a ranar kun 26 zuwa 27 a watan Afrilu.

A ranakun 3 da 4 na watan Mayu za a yi fafatawar zagaye na biyu.

A ranar 28 ga watan Mayu za a buga wasan karshe a filin San Siro na AC Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.