Isa ga babban shafi
Wasanni

Nadal ya shigar da karar Minista a Kotu

Gwarzon dan wasan Tennis da ke a matsayi na biyar a duniya, Rafael Nadal ya shigar da karar tsohuwar ministar lafiya da wasanni ta kasar Faransa a kotu, bayan ta zarge shi da kwan-kwadon kwayoyi masu kara kuzari.

Gwarzan dan wasan Tennis Rafael Nadal
Gwarzan dan wasan Tennis Rafael Nadal Geoff Burke/USA Today Sport
Talla

Nadal mai shekaru 29 ya ce, ya shigar da karar Roselyne Bachelot ne saboda ya kare mutuncinsa da martabarsa a matsayinsa na dan wasa.

A watan jiya, ministar ta ce, Nadal ya yi fashin watanni bakwai ne a shekarar 2012 saboda gwajin da aka yi ma sa da ya nuna cewa ya kwankwadi kwayoyin,
amma shi ya ce, ya yi fashin ne saboda rashin lafiya.

Roselyne mai shekaru 69 ta rike mukamin ministan ne a zamanin tsohon shugaban Faransa Nicholas Sarkozy.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.