Isa ga babban shafi
Wasanni

Akwai sauran aiki a gaban Leicester City

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City na neman maki biyu kafin ta samu nasarar lashe kofin gasar Premier ta bana.

Leicester City na neman maki biyu domin lashe gasar Premier ta Ingila.
Leicester City na neman maki biyu domin lashe gasar Premier ta Ingila. Reuters / Eddie Keogh Livepic
Talla

Wannan kuwa na zuwa ne byan ta gaza samun maki uku a fafatawar da ta yi da Manchester United a Old Trafford a jiya Lahadi, inda suka tashi kunnen doki 1-1.

Akwai sauran aiki a gaban Leicester City wadda ke neman lashe gasar a karon farko tun bayan kafuwarta shekaru 132 da suka gabata.

To sai dai kungiyar za ta iya samun damar lashe gasar, idan dai Tottenham mai matsayi na biyu a teburin Premier ta gaza doke Chelsea a Stamford Bridge a fafatawar da za su yi a yau Litinin.

To idan dai Tottenham din ta samu nasara akan Chelsea, to hakan na nufin sai Leicester ta sake daura damara domin neman maki biyu a wasanni da za ta yi da Everton da Chelsea.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.