Isa ga babban shafi
Amurka

An fitar da Brazil a Copa America

Peru ta yi waje da Brazil a gasar Copa America bayan ta doke ta ci 1 da 0 a wasan da suka fafata a jiya Lahadi. Peru ce ta jagoranci rukuninsu na B kuma zata hadu ne da Colombia a kwata fainal.

Peru ta fitar da Brazil a Copa America
Peru ta fitar da Brazil a Copa America REUTERS
Talla

Brazil dai ta nemi kunnen doki ne domin samun nasarar tsallakewa amma idan har Ecuador ba ta ci wasanta ba.

Sai gashi kuma Ecuador ta casa Haiti 4 da 0, kuma yanzu za ta hadu ne da Amurka a kwata Fainal.

A yau Litinin ne Mexico za ta fafata da Venezuela, daga bisani Uruguay ta kece raini da Jamaica.

Mexico da Venezuela ne saman teburin rukuninsu na C da maki shida kuma sun tsallake zuwa zagaye na gaba bayan sun samu nasara a wasanni biyu da suka buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.