Isa ga babban shafi
Wasanni

Kashi 70 na 'yan wasan Rasha zasu fafata a Olympics-IOC

Shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar Rasha Alexander Zukhov ya bada tabbacin cewa kwamitin kula da gasar na duniya IOC ya wanke yan kasar 271 daga zargin shan kwayoyin karin kuzari.

Shugaban kasar Rasha yana jawabi ga tawagar kasar a wasannin olympics
Shugaban kasar Rasha yana jawabi ga tawagar kasar a wasannin olympics
Talla

Daga cikin masu wakiltar kasar Rashan da aka wanke akwai yan dambe guda 11, sai tawagar yan wasan Judo, sai kuma masu wasan Volley ball guda 30.

A daren da ya gabata ne Kwamitin na IOC ya sanar da wannan mataki.

Tun farko dai tawagar ‘yan wasan da zasu wakilci Rashan zuwa gasar ta Olympics na kunshe da yan wasa 387 sai dai zargin da akai wa wasu daga cikin masu wakiltar kasar kan shan kwayoyin kara kuzari yasa a rage yawanzu zuwa 271.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.