Manchester United ta sha kashi sau uku a jere
Manchester United ta sha kashi sau uku a jere a cikin kaka guda, bayan da Watford ta casa Manchester United da ci 3-1 a karawar da suka yi jiya a gasar Primiya ta Ingila.
Wallafawa ranar:
A karo na farko kenan tun shekarar 2002 da kocin Manchester United, Jose Mourinho ke shan irin wannan kashin a tarihinsa na tamaula.
A karawar da ta yi da Manchester City, Manchester United ta kashi da ci 2-1 yayin da Feyenoord ta yi mata ci daya mai ban haushi a gasar Europa a ranar Alhamis.
Tuni dai masu lura da harkokin wsanni a duniya suka fara diga ayar tambaya kan Mourinho, musamman ma idan aka yi la’akari da ‘yan wasan da siyo a wannan kakar.
Sai dai Mourinhio ya ce, za su gyara kuma babu tantama a kan haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu