Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho zai sake ajiye Rooney a banci

Akwai yiwuwar kocin Manchester United, Jose Mourinho ya sake ajiye kaften dinsa Wayne Rooney a banci a fafatawar da kungiyar za ta yi da Zorya Luhansk ta Ukraine a gasar Europa League a gobe Alhamis.

Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney
Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney Action Images/Reuters/Carl Recine
Talla

Kocin dai ya ajiye Rooney a banci a wasan da Manchester United ta doke Leicester city da ci 4-1 a gasar Premier ta Ingila da suka yi a karshen makon jiya.

Ana dab da kammala wasan ne, Manchester United ta sanya kyaften din nata.

A hirar da ya yi da ‘yan jaridu a yau Laraba, Jose Mourinho ya ce, Rooney na ckin tawagar da za ta yi masa wasan na gobe, amma babu tabbacin cewa, da shi za a fara wasan.

Tun lokacin da aka nada Mourinho a matsayin koci, aka fara hasashen makomar Wayne Rooney a Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.