Tsohon Kaftin na Brazil Carlos Alberto ya rasu
Carlos Alberto tsohon Kaftin na ‘Yan kwallon kafar kasar Brazil da suka lashe kofin duniya a 1970 ya rasu a yau Talata yana da shekaru 72 a duniya. Rahotanni sun ce ya rasu ne a birnin Rio sakamakon bugun zuciya.
Wallafawa ranar:
Carlos Alberto ya yi zamani ne tare da Pele wadanda suka jagoranci tawagar Brazil da suka doke Italiya ci 4-1 a wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Mexico 1970.
A birnin Rio aka haifi Alberto Carlos a shekarar 1944, sannan ya buga wasa da Pele a kungiyar Santos tsakanin 1966 zuwa 1974.
Sannan ya buga wasa a kungiyar New York Cosmos a tsakanin 1977 zuwa 1980.
Alberto Carlos ya koma aikin horar da 'yan wasa bayan ya yi rataye takalmin kwallon shi a 1982. Ya horar da Flamengo ta Brazil da kuma kungiyoyi a Colombia da Mexico da Oman da Azerbaijan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu