An mika wa Chapecoense kofin Sudamericana
Hukumar kwallon kafar kudancin Amurka ta bai wa kungiyar Chapecoense kofin gasar Copa Sudamericana bayan akasarin 'yan wasan kungiyar sun gamu da ajalinsu a hatsarin jirgin sama da ya ritsa da su a Colombia.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan wasan kungiyar 19 ne suka rasa rayukansu a hatsarin na makon jiya kuma a dai dai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wasan karshe a gasar, in da suka yi shirin kece raini da Atletico Nacional.
Kungiyar Atletico Nacional ce ta bukaci a mika kofin ga Chapacoense, lura da lamarin ban tausayi da ya cika da ‘yan wasan.
A bangare guda, kimanin mutane 13 ne cikin kwanaki biyu, suka nemi a dauke su don ci gaba da buga wa Chapecoense kwallon kafa da ke Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu