Isa ga babban shafi
Wasanni

Gabon ta kira Ndong don buga mata gasar Afrika

Kasar Gabon ta kira dan wasanta da ke taka leda a Sunderland, Didier Ndong don buga mata gasar cin kofin Afrika da za ta karbi bakwanci a cikin watan Janairu mai zuwa.

Dan wasan Gabon, Didier Ndong
Dan wasan Gabon, Didier Ndong sportsmole.co.uk
Talla

A cikin watan jiya ne kasar ta yi watsi da dan wasan bayan ya ki halartar horo gabanin wasan da ta yi da Mali a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Gabon dai, ita ce kasar farko a Afrika da ta bayyana sunayen ‘yan wasa 23 da za su buga mata gasar, kuma a ranar 14 ga watan gobe ne za ta yi wasan share fage tare da Guinea Bissau.

Dole ne kasashen da za su buga wannan gasa su gabatar da sunayen ‘yan wasansu kafin nan da ranar 4 ga watan gobe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.