FIFA ta amince da kasashe 48 a gasar kofin duniya
Hukumar kwallon kafa ta duniya ta amince da matakin fadada gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa duk bayan shekaru hur-hudu, in da daga shekarar 2026, kasashen duniya 48 za su rika fafatawa a babbar gasar.
Wallafawa ranar:
A yau Talata ne mambobin hukumar ta FIFA suka kada kuri’ar amincewa da kudirin wanda shugaban hukumar Gianni Infantino ya gabatar.
Yanzu haka dai za a rika gudanar da jumullar wasanni 80 a gasar a maimakon 64 da aka saba yi, in da kasashe 32 ke fafatawa da juna.
Kazalika za a rika kammala gasar ta cin kofin duniya a cikin kwanaki 32 da zaran an fara aiwatar da matakin.
A karo na farko kenan tun shekarar 1998 da aka fadada gasar cin kofin duniya, abin da zai bai wa kasashen da ba su taba halarta ba a can baya, damar shiga domin a dama da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu