Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta kai wasan karshe na Copa del Rey

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tsallaka matakin wasan karshe a gasar cin kofin Copa del Rey duk da cewa sun tashi kunnen doki 1-1 da Atletico Madrid a fafatawar da suka yi a jiya a Camp Nou.

Luis Suarez ya ci wa Barcelona kwallo a fafatawarsu da Atletico Madrid a gasar Copa del Rey
Luis Suarez ya ci wa Barcelona kwallo a fafatawarsu da Atletico Madrid a gasar Copa del Rey Reuters/Albert Gea
Talla

To amma idan aka hada da sakamakon wasansu na farko, jumullar kwallaye 3 kenen Barcelona ta samu yayin da Atletico Madrid ke da kwallaye 2.

Luiz Suarez ne ya ci wa Barcelona kwallon a minti na 43 duk da cewa an kore shi daga filin wasan bayan an ba shi jan kati.

Kevin Gameiro na Atletico Madrid ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaren gida kafin daga bisani ya samu damar zura kwallo a ragar Barcelona a minti na 83.

Yanzu dai Barcelona mai rike da kambin gasar ta Copa del Rey za ta hadu da Alaves ko kuma Celta Vigo a wasan karshe.

Wadannan kungiyoyi biyu za su fafata a matakin wasan dab da karshe a yau Laraba, kuma wadda ta yi nasara ne za ta hadu da Barcelona a wasan karshe.

Luiz Suarez dai ba zai buga wa Barcelona wasan karshen ba saboda jan katin da aka ba shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.