Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona na cikin tsaka mai wuya

Wasu daga cikin masu sharhi kan wasan kwallon kafa sun ce akwai aiki babba a gaban ‘yan wasan gaba na Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, wato Neymar, Suarez da kuma Messi wajen zurawa kungiyarsu kwallaye a ragar Juventus a ranar 19 ga watan Afrilu don kaiwa mataki na gaba a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Dan wasan kungiyar Barcelona Lionel Messi da Giorgio Chiellini na Juventus yayain wasan da suka fafata a ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2017 a kasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
Dan wasan kungiyar Barcelona Lionel Messi da Giorgio Chiellini na Juventus yayain wasan da suka fafata a ranar 11 ga watan Afrilu shekarar 2017 a kasar cin kofin zakarun nahiyar turai. Reuters / Giorgio Perottino Livepic
Talla

Kungiyar Juventus ta lallasa Barcelona da 3-0 a zagayen farko na wasan da suka a buga a birnin Turin na Italiya a talatar da ta gabata, ta hannun ‘yan wasanta Dybala da ya zura kwallaye 2 da Giorgio Chiellini.

Tun bayan fara wgasar ta cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, su biyu kawai aka samu nasarar jefawa kungiyar Juventus kwallo a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.