Man U da City sun rike juna a Etihad
Manchester United da Manchester City sun rike juna babu ci a tsakaninsu a fafatawar da suka yi a gasar Firimiya daren jiya Alhamis. Fafatawar dai ta kasance ta neman samun hurumin shiga gasar zakarun Turai tsakanin Mourinho na United da Guardiola City.
Wallafawa ranar:
City ta kasa cin United duk da jan katin da aka ba Fellaini ana saura minti 6 a hure wasan.
Yanzu dai City na matsayinta na hudu, da tazarar maki guda tsakaninta United da ke matsayi na 5. Amma dukkaninsu suna da kwanten wasa guda.
Manchester United dai na iya shiga gasar zakarun Turai idan har ta lashe kofin gasar Europa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu