Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan da suka mutu kan ganiyar kwallon kafa

Tsohon dan wasan Newcastle kuma dan asalin kasar Ivory Coast, Cheik Tiote ya rasu yana da shekaru 30 bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin atisaye da kungiyarsa ta Beijing Enterprise da ke China. Sakamakon wannan rasuwa ta Tiote, mun yi dubi game da wasu ‘yan wasa da suka mutu a lokacin da suke ganiyar sana’arsu ta kwallon kafa. 

Cheick Tioté, dan wasan baya-bayan nan da ya rasu a China
Cheick Tioté, dan wasan baya-bayan nan da ya rasu a China ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

A cikin watan Yunin shekarar 2003 ne, dan wasan tsakiya na Kamaru Marc Vivien Foe ya rasa ransa sakamakon bugun zuciya a lokacin wasansu da Colombia a gasar FIFA ta cin kofin kalubale a Faransa da aka fi sani da Confederation Cup.

Foe ya rasu yana da shekaru 28 kuma ya buga kwallo a Manchester City da West Ham da kuma Lyon.

Akwai kuma Antonio Puerta na Spain da ya rasu a watan Agustan 2007 bayan kwanaki uku da ya yanke jiki ya fadi a daidai lokacin da ya ke buga wa kungiyarsa ta Sevilla gasar La Liga da Getafe.

Bincike ya nuna cewa, dukkanin gabobinsa sun daina aiki saboda bugun zuciya kuma ya rasu ne watanni uku da jagorantar Sevilla har ta lashe gasar UEFA.

Sai kuma dan wasan Motherwell Phil O’Donnell da ya rasu a watan Disamban 2007 sakamakon bugun zuciya da ya ritsa da shi a yayin buga wa kungiyarsa wasa a gasar Premier ta Scotland.

Dan wasan mai shekaru 35 ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin da ake shirin sauya shi da wani dan wasan.

A cikin watan Agustan shekarra 2009 ne, dan wasan Espanyol Daniel Jarque ya gamu da ajalinsa bayan zuciyarsa ta buga a wani dakin Otel gabanin wasansu na share fagen kaka da Coverciano a Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.