Isa ga babban shafi
wasanni

"Kar a tilasta wa Enyeama komawa Super Eagles"

Tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida ya ce, kar a kuskura a tirsasa wa Vincent Enyeama dawowa cikin tawagar Super Eagles don tsaren raga a gasar cin kofin duniya a Rasha bayan ya yi ritaya shekaru biyu da suka wuce.

Vincent Enyeama tare da  Lionel Messi na Argentina a wani sada da suka yi a shekarun baya
Vincent Enyeama tare da Lionel Messi na Argentina a wani sada da suka yi a shekarun baya Pedro Ugarte/AFP
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kiraye kirayen ganin cewa, an maido da kwararren golan don tsare wa Najeriya raga a babbar gasar ta  kwallon duniya.

A cewar Babangida, tabbas, Enyeama kwararren gola ne amma bai kamata a tilasta ma sa janye ritayarsa ba, a maimakon haka, Super Eagles ta mayar da hankali wajen horar da matasan masu tsaren gida na tawagar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.