Kane ya bayyana farin ciki bisa sanya shi a sahun Messi da Ronaldo
Dan wasan gaba na kungiyar Tottenham, kuma na tawagar kasar Ingila Harry Kane, ya bayyana farin ciki ganin yadda a yanzu aka sanya shi a sahun shahararrun ‘yan wasa kamar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo, bayan da yaci kwallaye uku a wasan da suka lallasa Southampton da 5-2.
Wallafawa ranar:
Wannan nasara ta bai wa Kane damar zama dan wasa na farko a nahiyar turai, tun bayan shekarar 2009, da zai kammala kakar wasa da kwallaye 56 da ya ci wa kungiyarsa da kasarsa, rabon da a samu haka kuwa tun bayan Messi (54) da Ronaldo.
Zalika Harry Kane goge tarihin shekaru 22 da tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya kafa a gasar Premier na cin kwallaye 36 a kakar wasa guda a lokacin da yake bugawa kungiyar Blackburn Rovers inda a yanzu ya ke da kwallaye 39.
A cewar Harry Kane kwatanta kwazonsa da na Messi da Cristiano ba kamar nasara bace a gareshi, wadda kuma zai yi amfani da ita, wajen bashi kwarin gwiwa a shekara ta 2018 mai kamawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu