Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya zata buga wasannin sada zumunci da kasashe 5

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta sanar da karin wasannin sada zumunci guda uku da tawagar kwallon kafa ta kasar Super Eagles zata buga, kafin fara gasar cin kofin duniya a Rasha cikin wannan shekara.

Nigerian Super Eagles Team
Nigerian Super Eagles Team Reuters/Peter Cziborra
Talla

Kasashen da Super Eagles zasu fafata da su, sun hada da kasar Serbia a ranar 27 ga watan Mayu a birnin London, sai kuma Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo wadda Najeriya zata karbi bakuncinta a Abuja ko Uyo, a ranar 28 ga watan na Mayu.

Wasan sada zumuncin tsakanin Najeriya da kasar Czech kuwa zai gudana ne a ranar 6 ga watan Yuni mai zuwa.

Kafin wannan sanarwar, hukumar ta NFF ta ce Najeriya zata buga wasannin sada zumunci tsakaninta da kasashen Poland da kuma Ingila a ranakun 23 ga watan Maris da kuma 2 ga watan Yuni.

Najeriya na cikin rukuni na hudu, tare da kasashen Crotia, Iceland da kuma Argentina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.