Isa ga babban shafi
Wasanni

Antonio Conte zai fuskanci tsigewa

Akwai yiwuwar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sanar da matsaya kan kocinta Antonio Conte a yau, matsayar da ake ganin za ta kai ga sallamar kocin daga bakin aiki, biyo bayan rashin nasarar da club din ke ci gaba da fuskanta a gasar Pirimiya.

Antonio Conte ya sha musanta rade-radin korarsa daga bakin aiki sakamakon rashin nasarar Club din a baya-bayan nan.
Antonio Conte ya sha musanta rade-radin korarsa daga bakin aiki sakamakon rashin nasarar Club din a baya-bayan nan. Reuters/Alessandro Garofalo
Talla

Bayan kada kuri’ar yankan kaunar da Conte ya bukaci kadawa a jiya, sakamo ya nuna cewa Club din zai iya sallamar Conte daga bakin aiki.

Rahotanni dai sun nuna cewa Club din ya fuskanci rashin nasarar da bai taba fuskanta ba a lokacin jagorancin Conte tun bayan rashin nasararta a shekarar 1995.

Ko da ya ke dai har yanzu Conte yaki amincewa da hasashen da ake da shi kansa na cewa za a iya sallmarsa daga Club din, sai dai ya ce cikin farin ciki zai karbi duk wani mataki da Club din ya yanke a kansa.

Watanni 18 ya rage kafin cikar wa'adin kwantiragin Conte a Chelsea, sai dai yana fatan kara tsawaita kwantiragin gabanin karewarsa duk da jerangiyar rashin nasarar da Club din ke fuskanta a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.