Isa ga babban shafi
wasanni

Real Madrid ta tsallaka matakin gaba a gasar zakarun Turai

Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid mai rike da gambi ta tsallaka matakin wasan dab da na kusan krshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai bayan ta samu nasarar casa PSG da ci 2-1 a filin wasa na Parc des Princes.

Christiano Ronald ya taimakawa Real Madrid shiga matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar zakarun Turai
Christiano Ronald ya taimakawa Real Madrid shiga matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar zakarun Turai PIERRE-PHILIPPE MARCOU / AFP
Talla

Christiano Ronaldo ne ya fara zura kwallon farko a minti na 51 a ragar PSG kafin daga bisani Edison Cavani ya farke a minti na 71.

Sai dai a minti na 80, Casemiro ya sake ci wa Madrid kwallo ta biyu.

A jumulce dai, Madrid na da kwallaye biyar da ta zura a ragar PSG idan aka hada da fafatawarsu ta farko a Santiago Bernabeu, yayin da PSG ke da kwallaye biyu.

A karo na biyu kenan a jere da ake yin waje da PSG a matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun Turai duk da cewa ta bada tazarar maki 14 a teburin gasar Lig 1 ta Faransa da ta ke jagoranta.

Yanzu haka dai, makomar kocin PSG, Unai Emery na cikin halin rashin taabbas duk da cewa tun shekarar 2016 ya ke horar da ‘yan wasanta.

Ita kuwa Liverpool ta tashi babu ci a karawar da ta yi da FC Porto a Anfield.

Sai dai Liverpool na da jummullar kwallaye biyar da ta jefa a ragar FC Porto idan aka hada da wasansu na zagayen farko, in da Porto ta tashi a tutar babu.

To a karon farko kenan tun shekarar 2009 da Liverpool ke samun nasarar tsallakawa matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar ta zakarun nahiyar Turai.

Nan da ranar 16 ga wannan watan ne, Liverpool za ta san kungiyar da za ta kara da ita a matakin gaba na gasar ta zakarun Turai bayan an fitar da sabon jadawali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.