wasanni
Manchester United na shirin siyar da Pogba
Wasu rahotanni daga Birtaniya na cewa, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na da muradin siyar da tsadadden dan wasanta, wato Paul Pogba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Wannan dai na zuwa ne bayan wasu bayanai na cewa, Pogba da kocinsa, Jose Mourihno na nesa da juna wajen hulda tun bayan da kungiyar ta ajiye shi a banci a watan jiya.
Daga cikin wadanda ake ganin Manchester United za ta karkata hankalinta don kulla kwantiragi da su, sun hada da Raphael Varane na Real Madrid da Toni Kroos na Jamus da kuma Marquinhos na PSG har ma da Alex Sandro na Juventus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu