Isa ga babban shafi
Wasanni

Welbeck ya cira wa Arsenal kitse a wuta

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya jinjina wa kaifin basirar dan wasansa Danny Welbeck sakamakon yadda ya cire wa kungiyar kitse a wuta a fafatawar da suka doke West Ham da ci 3-2 a gasar firimiyar Ingila a jiya Lahadi.

Danny Welbeck na Arsenal
Danny Welbeck na Arsenal REUTERS
Talla

Welbeck da ya zura kwallaye biyu a minti na 38 da 81, ya kuma taimaka wajen zura kwallon da Pierre- Emerick Aubameyang ya jefa a ragar Southampton a minti na 28.

Wenger ya bayyana fafatawar ta jiya a matsayin mai matukar wahala saboda a cewarsa, sun kara ne da kungiyar da ta jajirce don ganin ba a samu nasara akan ta ba.

Sau bakwai dai Wenger na saauya ‘yan wasansa a karawar, in da ake ganin ya yi haka ne don taka-tsan-tsan kan wasan da za su yi da CSKA Moscow a ranar Alhamis mai zuwa a gasar Europa League.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.