Isa ga babban shafi
Wasanni

Ancelotti yayi watsi da tayin horar da tawagar kwallon kafar Italiya

Shahararren mai horar da wasan kwallon kafa Carlo Ancelotti ya ki amincewa da tayin da akai masa na karbar ragamar horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Italiya.

Tsohon mai horar da Kungiyar Bayern Munich Carlo Ancelotti.
Tsohon mai horar da Kungiyar Bayern Munich Carlo Ancelotti. REUTERS/Charles Platiau/File Photo
Talla

Tawagar kwallon kafar Italiya sun kwashe tsawon lokaci ba tare da mai horarwa na dindindin ba, tun bayanda hukumar kwallon kafa ta kasar ta kori tsohon kocin tawagar Gian Piero Ventura.

Ventura ya rasa mukaminsa ne sakamakon rashin nasarar da Italiya ta yi na samun tikitin halartar gasar cin kofin duniya da za’a yi a Rasha, karo na farko cikin shekaru 60.

A makon da ya gabata ne akarawaito cewa Ancelotti, wanda kungiyar Bayern Munich ta kora awatan Satumba, ya gana wakilan hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya a birnin Rome.

Sai dai daga bisani Ancelotti yayi watsida tayin, a dai dai lokacinda ake hasashen mai yiwuwa ne ya maye gurbin Arsene Wenger a karkashen kakar wasa ta bana, bayan ajiye aikin horar da kungiyar Arsenal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.