Isa ga babban shafi
Wasanni

Iniesta zai maye gurbin mukamin Arteta a Manchester City

Tsohon dan wasan tsakiya na Barcelona Andres Iniesta, na kan gaba a tsakanin wadanda ake sa ran zasu maye gurbin Mikel Arteta a matsayin mataimakin kocin Manchester City Pep Guardiola.

Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta.
Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta. Reuters/Paul Hanna
Talla

Guardiola na fatan maye gurbin Arteta ne, bayan da ta tabbata cewar wani lokaci nan gaba, za a tabbatar da shi a matsayin sabon mai horar da kungiyar Arsenal.

Tuni dai wakilan kungiyar Manchester City suka fara tattaunawa da Iniesta, wanda ake sa ran zai amince da tayin.

Bayan yanke shawarar dakatar da wasa a Barcelona, Iniesta mai shekaru 34, ya ce zai koma buga wasanni ne a kungiyoyin da ke wajen nahiyar turai domin kaucewa fuskantar tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona a wasanni na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.