Isa ga babban shafi
wasanni

Iniesta zai koma Japan da taka leda

Bisa dukkan alamu, Andres Iniesta ya shirya komawa kungiyar kwallon kafa ta Vissel Kobe da ke Japan bayan ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, zai koma sabon gidansa tare da abokinsa Hiroshi Mikitani, wato mamallakin kungiyar ta Japan.

Andres Iniesta ya shafe shekaru 22 a Barcelona
Andres Iniesta ya shafe shekaru 22 a Barcelona REUTERS/Albert Gea
Talla

Iniesta mai shekaru 34 ya wallafa hotonsa da Mikitani a cikin wani karamin jirgin sama, sannan kuma ga hoton tutar Japan da kuma kwallon kafa a gefe.

Kungiyar ta Vissel Kobe ta sanar cewa, za ta gudanar da wani taron manema labarai don kaddamar da wani sabon dan wasanta, amma ba ta fadi sunan dan wasan karara ba, sai dai ana kyautata zaton Iniesta ne.

A cikin watan jiya, Iniesta ya sanar cewa, zai raba gari da Barcelona a karshen kakar bana, bayan ya shafe shekaru 22 yana murza mata tamaula.

Iniesta ya lashe kofin zakarun Turai guda hudu, da kofin La Liga guda takwas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.