Isa ga babban shafi
wasanni

Ronaldo zai sanar da makomarsa a Real Madrid

Christiano Ronaldo ya ce, nan kusa zai sanar da makomarsa a kungiyar Real Madrid bayan ya taimaka ma ta daukan kofin gasar zakarun Turai karo na uku a jere.

Cristiano Ronaldo ya taimaka wa Real Madrid daukan kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere
Cristiano Ronaldo ya taimaka wa Real Madrid daukan kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere REUTERS/Paul Hanna
Talla

Ko da yake Ronaldo bai zura kwallo a wasan na karshe da suka dole Liverpool da ci 3-1 ba a raanar Asabar, amma, ya kammala kakar gasar ta bana da kwallaye 15 da ya jefa a raga, in da ya kasance dan wasa mafi yawan kwallaye a kakar gasar ta bana.

Ronaldo ya ce, nan da ‘yan kwanaki kalilan masu zuwa zai bayyana wa magoya bayansa makomarsa a Real Madrid.

Dubun dubatan magoya bayan kungiyar sun yi jerin gwano a titunan babban birnin Spain don jinjina wa ‘yan wasan kungiyar bayan dawowarsu daga birnin Kiev a jiya Lahadi, in da wasan karshe ya gudana.

Real Madrid ta lashe kofin ne karo na uku a jere, amma karo na 13 a jumulce.

Magoya bayan sun yi ta sowa tare da daga kyallaye a daidai lokacin da wata katuwar mota ke zagayawa da ‘yan wasan da kuma kofin da suka lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.