Isa ga babban shafi
Wasanni

Serena ta kai zagayen kusa da na karshe a gasar Wimbledon

Serena Williams ta samu kai wa zagayen kusa da na karshe ne a gasar kwallon tennis ta Wimbledon da ke gudana a birnin London, bayan samun nasara akan Camila Giorgi ta Italiya da kwallye 6-3, 6-4 sai kuma 3-6, a wasan gaf da na kusa da karshe da suka fafata a ranar Laraba, 11 ga watan Yuli na 2018.

Serena Williams, bayan samun nasarar kai wa zagayen kusa da karshe na gasar Wimbledon.
Serena Williams, bayan samun nasarar kai wa zagayen kusa da karshe na gasar Wimbledon. AFP Photo/Oli SCARFF
Talla

A halin yanzu Serena za ta fafata ne da Julia Goerges ‘yar kasar Jamus a wasan kusa da na karshe.

Idan har Serena Williams ta yi nasara to za ta ta jira wanda zai samu nasara ne tsakanin Angelique Kerber da kuma Jelena Ostapenko don fafatawar wasan karshe na gasar ta Wimbledon da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Serena Williams dai ta taba lashe wannan gasar tennis din ta Wimbledon sau 7 a baya.

Wani abin daukar hankali a gasar kwallon tennis din ajin mata a gasar ta Wimbledon, shi ne yadda ‘yan wasa 3 daga cikin 4 da suka kai zagayen kusa da na karshe a gasar, dukkaninsu zakaru ne a gasar ta kwallon Tennis.

‘Yan wasan sun hada da Serena Williams, wadda taba lashe kofin gasar ta Wimbledon sau 7, Angelique Kerber ta kasar Jamus, wadda ta lashe kofunan gasar Australian da US Open a shekarar 2016, da kuma Jelena Ostapenko ‘yar kasar Latvia mai rike da kofin gasar French Open da aka yi a farkon 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.