Angelique Kerber ta doke Serena Williams
Serena Williams da aka sa ran za ta kafa sabon tarihi a gasar kwallon Tennis na gasar Wimbledon ta bana da ke gudana a birnin London,ta yi kasa a gwiwa a karawarta da Angelique Kerber yar kasar Jamus.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A yau Asabar Serena Williams da ke jego, ta fafata da Angelique Kerber ‘yar kasar Jamus a wasan karshe, watanni 10 kacal bayan haihuwa da ta yi a watan Satumba na shekarar 2017.
Manazarta sun sa ran cewa Serena za ta samu wannan nasara wanda hakan zai zama karo na farko da mai jego ta lashe kofi a daya daga cikin manyan wasannin kwallon tennis cikin shekaru 38, bayan tarihin da Evonne Googlagong ta kafa.
A shekarar 1980 Evonne Googlagong ‘yar kasar Australia, ta kafa tarihin zama mai jego ta farko da ta lashe kofin babbar gasar Tennis a duniya.
A karawar ta yau Angelique Kerber yar kasar Jamus ta doke Serena Williams da ci 6-3, 6-3 bayan share kusan sa'o'i daya ana karawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu