Na yi nadamar horar da Arsenal- Arsene Wenger
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce, shafe tsawon shekaru 22 a wannan kungiya, shi ne babban kuskuren da ya tafka a ruyuwarsa. A cewarsa, ya yi nadamar sadaukar da komai saboda kungiyar.
Wallafawa ranar:
Wenger mai shekaru 68 ya karbi aikin horar da Arsenal ne a cikin watan Oktoban shekarar 1996, yayin da ya raba gari da ita a karshen kakar wasannin da ta gabata.
A wata hira da jaridar Farana ta RTL, Wenger ya ce, zai tsayar da shawara kan makomarsa nan da wasu ‘yan watanni masu zuwa.
A yayin da aka tambaye shi game da babbar kuskurensa a rayuwa, sai kocin ya ce, “ watakila zama a kungiya guda har tsawon shekaru 22”
"Ni mutum ne mai son sabbin abubuwa, mai son sauye-sauye, amma duk da haka ina son fuskantar kalulabe .” in ji Wenger.
Tsohon kocin ya kara da cewa, “ Na yi nadamar sadaukar da komai saboda kungiyar domin na gano cewa, na cutar da makusantana da dama.”
“Na yi watsi da mutane da dama . Na yi watsi da iyalina” in ji Bafaranshen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu