Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta tuntube ni - Willian

Dan wasan gaba na Brazil da ke bugawa kungiyar Chelsea, Willian Borges da Silva, ya ce babu shakka kungiyar Barcelona ta tuntube shi dangane da yiwuwar barin Chelsea zuwa gare ta, labarin da aka jima ana tantamar sahihancinsa.

Dan wasan gaba na Chelsea Willian, yayin gaisawa da Lionel Messi na Barcelona, bayan fafatawa a wasan gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, wanda aka tashi 1-1. 20 ga watan Fabarairu, 2018.
Dan wasan gaba na Chelsea Willian, yayin gaisawa da Lionel Messi na Barcelona, bayan fafatawa a wasan gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, wanda aka tashi 1-1. 20 ga watan Fabarairu, 2018. Andrew Boyers/Reuters
Talla

Willian mai shekaru 29, ya bada tabbacin ne, bayan da suka yi rashin nasarar lashe kofin gasar ‘Community Shield’ a wasan da suka fafata da Manchester City.

A cewar dan wasan, zai ci gaba da zama tare da Chelsea, sai dai idan kungiyar ce ba ta bukatar ya ci gaba da kasancewa tare da ita.

A baya dai an sha alakanta Willian da yiwuwar sauyin sheka zuwa kungiyoyin Real Madrid, da kuma Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.