Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyoyi a Najeriya za su buga wasannin Premier 8 cikin wata guda

Masu horar da kungiyoyi, magoya baya da kuma ‘yan wasan da ke bugawa kungiyoyin kwallon kafa da ke buga gasar Premier League ta Najeriya sun koka bisa yawan wasannin da za su buga cikin gajeren wa’adi.

'Yan wasa, da masu horar da kungiyoyin kwallon kafa da ke Najeriya sun koka bisa gajeren wa'adin kammala gasar Premier ta kasar.
'Yan wasa, da masu horar da kungiyoyin kwallon kafa da ke Najeriya sun koka bisa gajeren wa'adin kammala gasar Premier ta kasar. SCORE NIGERIA
Talla

Koken dai ya biyo bayan lafawar da kura ta yi dangane da rikicin shugabancin hukumar kwallon kafar Najeriyar NFF, tsakanin Amaju Pinnick da Chris Giwa.

An dai shafe kusan shekru hudu ana takaddama kan sahihin shugaban hukumar ta NFF, tsakanin Giwa da Pinnick abinda ya sa FIFA yin gargadin haramtawa Najeriya da ma jami’anta shiga, ko gudanar da wasanni a cikin gida, nahiya da ma kasa da kasa.

A halin yanzu dai Najeriya ta fice daga wannan barazana ta fuskantar fushin FIFA, bayan da mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da bangarorin masu rikici da juna da kuma sauran masu ruwa da tsaki, inda ya tabbata Amaju Pinnick ne zai ci gaba da kasancewa shugaban hukumar kwallon ta Najeriya.

Nasarar kawo karshen rikicin ya sa wasannin Najeriyar da suka dakata a matakin kasa tsawon watanni 2, za su ci gaba da gudana, ciki har da gasar Premier League wadda rikicin shugabancin NFF ya fi haddasawa koma baya.

Tuni dai hukumar LMC da ke shirya gasar Premier ta Najeriya ta tsayar da ranar 2 ga watan Satumba a matsayin lokacin da wasannin gasar za su ci gaba, sai kuma ranar 28 ga watan Oktoba lokacin da za’a rufe gasar.

Sai dai masu iya magana sun ce ba’a nan gizo ke sakar ba, domin kuwa jadawali ko wa’adin da aka debawa karashen gasar ta Premier ya nuna cewa kowace kungiya za ta buga wasannin gasar kadai har guda 8 a cikin wata guda, a gefe guda kuma akwai sauran wasanni na gasar cin kofin AITEO da kungiyoyin za su buga.

Sai dai duk da wannan kalubale, da alama babu wani zabi ga kungiyoyin Najeriyar face rungumar kaddara, la’akari da cewa hukumar LMC da ke shirya gasar Premier ta kasar, ta gajarce wa’adin buga wasannin ne, bisa umarni da sabon tsarin hukumar kula da kwallon kafar nahiyar Afrika, wadda ta ce daga yanzu, sabuwar kakar wasanni a kowace kasa za ta soma ne a kowane watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.