Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar ya samu rauni a kafar da ya taba karyewa

Mai horar da kungiyar PSG Thomas Tuchel, ya ce sun shiga damuwa ainun sakamakon raunin da dan wasansu na gaba Neymar ya samu a idon sawunsa, yayin wasan 'Coupe de France', gasar cin kofin Faransa da PSG ta lallasa Strasbourg da 2-0.

Dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, bayan samun rauni a kafar da ya taba karyewa.
Dan wasan gaba na kungiyar PSG Neymar, bayan samun rauni a kafar da ya taba karyewa. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Raunin da Neymar ya samu ya tilasta masa ficewa daga wasan nasu da Strasbourg a mintuna na 60, yana mai matsar kwalla.

Wannan koma baya na neman fuskanto kungiyar ta PSG ne, yayinda ya rage makwanni 3 su yi tattaki zuwa filin Old Trafford, domin fafatawa da Manchester United a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Neymar wanda ya ci wa PSG kwallaye 20 a dukkanin wasannin da ya buga mata a kakar wasa ta bana, ya sake samun rauni ne a kafar da ya taba samun karaya cikin watan Fabarairu na shekarar bara.

A halin yanzu ana dakon bayanin da likitoci za su fitar kan sabon raunin na Neymar kafin tantance zurfinsa.

Sai dai kocin kungiyar ta PSG, Thomas Tuchel, ya ce bai ji dadin kalaman da wasu, ‘yan wasan kungiyar Starsbourg da kocinsu ke furtawa ba, na cewa salon wasan Neymar na gwaninta fiye da kima ke tsokano masa duka, la’akari da cewa wasan kurar da yakan yi da abokan karawarsa na harzuka su a lokuta da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.