Isa ga babban shafi
wasanni

Sami Khedira na Juventus zai shafe wata guda ya na jinyar zuciya

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta tabbatar da rashin lafiyar dan wasan tsakiyarta Sami Khedira, wanda ke fama da matsalar zuciya dai dai lokacin da Club din ke shirin tattaki zuwa Atletico Madrid a wasannin dab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai.

Dan wasan tsakiya na Juventus Sami Khedira
Dan wasan tsakiya na Juventus Sami Khedira reuters
Talla

Sanarwar da Club din ya fitar, ta ce tuni aka yi wa Khedira tiyata, sakamakon bugun zuciya cikin sauri da ya fuskanta lokacin da yake tsaka da atisaye a jiya Talata.

Da yake dan wasan zai shafe wata guda ya na jinya, hakan na nufin baya ga wasan yau da zai rasa, zai kuma rasa wasansu da Napoli a ranar 3 ga watan Maris baya ga zagaye na biyu na wasan dab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai tsakaninsu da Atletico a ranar 12 ga watan na Maris.

Khedira dai za a iya cewa bai faro wannan kaka da sa a ba, don kuwa wasanni 15 kacal ya iya bugawa sakamakon cutukan da ya rika fuskanta, ciki har da raunin watan Satumba da ya samu a kugu wanda ya dauke shi makwanni 5 ya na jinya, sai kuma na watan Nuwamba ka nan a yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.