Isa ga babban shafi
Wasanni

Mourinho yayi tsokaci kan kalubalen da Real Madrid ke fuskanta

Tsohon mai horar da Manchester United Jose Maourinho, ya zargi Real Madrid da gazawa wajen nuna kwazon da ake bukata, a wasan El Clàsico da sauka fafata da Barcelona a ranar Asabar, 2 ga watan Maris.

Tsohon mai horar da Real Madrid Jose Mourinho.
Tsohon mai horar da Real Madrid Jose Mourinho. AFP/Thomas Coex
Talla

Mourinho, wanda ya taba horar da Real Madrid a shekarun baya, ya bayyana rashin jin dadin yadda wasannin tsakanin tsohuwar kungiyar tasa da Barcelona ya kaya, inda Madrid din ta sha kashi har sau biyu a haduwar da suka yi cikin kwanaki 4.

Kungiyoyin sun soma haduwa a wasan kusa da na karshe na gasar Copa del Rey inda Barcelona ta lallasa Madrid da kwallaye 3-0, sai kuma wasan La Liga da Barcelona ta yi tattaki har zuwa fillin wasa na Santiago Bernabeau ta samu nasara kan Real Madrid da 1-0.

Karo na farko kenan cikin shekaru 87, da Barcelona ta shiga gaban Real Madrid a jimillar wasannin da suka fafata da samun nasara kan juna, inda a yanzu kididdigar ta nuna cewa, Barcelona ta lallasa Madrid sau 96, yayinda ita kuma Real Madrid ta samu nasara kanta sau 95.

Zalika karo na farko kenan cikin shekaru 15, da Real Madrid ke shan kaye a hannun Barcelona har gida sau uku a jere.

Mourinho, wanda ke tsokaci kan halin da Real Madrid ta shiga na fuskantar kalubalen rashin nasarori, ya ce kungiyar ta rasa kwarjinin da ta shahara da shi a baya.

Jose Mourinho, na daga cikin masu horarwar da ake sa ran za su iya maye gurbin kocin Real Madrid na yanzu Santiago Solari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.